An kori jami'an gwamnatin Tanzania kan sace kudin girgizar kasa

An kori manyan jami'an gwamnati biyu
Bayanan hoto,

Girgizar kasar ta lalata wurare da dama

Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya kori manyan jami'an gwamnatinsa biyu bisa zargin sace kudin da aka ware domin taimakawa mutanen da wata girgizar kasa ta shafa.

Akalla mutum 16 ne suka mutu sannan mutum 200 suka ji rauni sakamakon girgizar kasar da aka yi a lardin Kagera ranar 10 ga watan Satumba.

Wata sanarwa da ofishin shugaban ya fitar ta ce mutanen sun bude wani asusun bogi domin a rika sanya kudin da aka ware na taimakawa mutanen.

Kazalika an dakatar da wani babban jami'in ajiyar kudi bisa zarginsa da hannu wajen kitsa sace kudin.

Bayanan hoto,

Girgizar kasar ta yi mummunar barna a birnin Bukoba

Kasashen waje sun bayar da nasu tallafin domin bai wa mutanen da girgizar kasar ta shafa.

Jaridar Citizen ta kasar ta ambato cewa ko da a ranar Talata sai da gwamnatin India $250,000 domin tallafawa mutanen da girgizar kasar ta shafa.