Ana neman agwagwar ruwan da ta ɓata daga Afirka ta kudu

Wasu masu rajin kare hakkin dabbobi ne suka sake ta

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Agwagwar ba za ta iya rayuwa sama da 'yan makonni ba

An kaddamar da gagarumin neman wani nau'i na agwagwar ruwa da ya kusa karewa a duniya, wanda wasu masu rajin kare hakkin dabbobi suka saka ba da son ransu ba.

Wasu dalibai ne a kasar Afirka ta kudu suka sace agwagwar a gidan kiwon dabbobi a wani mataki na nuna rashin yadda da tsare dabbobi a wuri daya.

An haifi agwagwar ne a gidan kiwon dabbobin, kuma ba za ta iya rayuwa a jeji ba.

Masana sun ce agwagwar ba za ta iya rayuwa fiye da makonni biyu a jeji ba.

Dylan Bailey, shugaban gidan kiwon dabbobin na Bayworld da ke Port Elizabeth, ya ce: "Agwagwar ba za ta iya rayuwa a jeji ba saboda ba zai san inda yake ba idan yana jeji. Abin farin ciki dai shi ne tana da koshin laifya, don haka za ta iya kai wa 'yan makonni a jeji ba tare da ta mutu ba shi ya sa ake nemanta."