Rasha ce ta harbo jirgin Malaysia samfurin MH17

Rasha ta ce ba ta da hannu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dukkan mutanen da ke jirgin sun mutu

Masu bincike na kasashen duniya da ke nazari kan jirgin sama mai lamba MH17 da ya fadi a gabashin Ukraine a shekarar 20014 sun ce makami mai linzamin da ya harbo shi ya fito ne daga yankin da ke karkashin ikon 'yan tawaye da Rasha ke mara wa baya.

Masu binciken sun kara da cewa an kai nau'rar da ke harba makami mai linzamin ne cikin Ukraine daga Rasha.

Dukkan mutum 298 da ke cikin jirgin samfurin Boeing 777 sun mutu lokacin da aka harbo shi a kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam daga Kuala Lumpur.

Iyalan mutanen da ke cikin jirgin sun shaida wa BBC cewa masu binciken sun gaya musu cewa za su yi bincike kan kusan mutum 100 game da faduwar jirgin.

Daya daga cikin iyalan mutanen da suka mutu Robby Oehler ya shaida wa BBC cewa, "Masu binciken sun gaya mana yadda aka kai nau'rar da ke harba makami mai linzamin da shaidun da suka nuna haka daga hotunan da aka dauka."

Kasar Jamus ce dai ta jagoranci binciken tare da hadin gwiwar Holland da Australia da Belgium da Malaysia da kuma Ukraine.