An hukunta mutumin da ya sato wa Buhari jawabi

An sauya wa mutumin wurin aiki

Asalin hoton, BERTRAND GUAY

Bayanan hoto,

Batun ya bai wa Najeriya kunya sosai

Gwamnatin Najeriya ta ce ta sauya wa mutumin da ya sato jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karanta a wajen wani taro na kaddamar da shirin gyara halayen 'yan kasar wurin aiki.

Mai magana da yawun fadar shugaban Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa an dauke mataimakin daraktan da ya rubuta jawabin, wanda aka sato wani bangare daga wani jawabin Shugaban Amurka, Barack Obama, daga Fadar Shugaban Kasa.

Mista Buhari ya kwafi jawabin ne a lokacin da ya ke kaddamar da shirin 'Gyara ya fara daga kaina' wanda gwamnatinsa ta bullo da shi.

Batun dai ya bai wa gwamnatin kasar kunya sosai musamman a daidai lokacin da shugaban kasar ke shirin zuwa Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.

Garba Shehu ya ce an tura mutumin zuwa ofishin sakataren gwamnatin kasar domin a sauya masa wurin aiki.

Wasu majiyoyi a Fadar Shugaban Kasar sun shaida wa wakilin BBC cewa an kirkiro wani bangare na musamman domin ya rika rubuta wa Shugaba Buhari jawabi, sannan an sayo wata na'ura da za ta rika gano dukkan bayanan da aka wanko daga wadansu jawaban.

Da ma dai Malam Garba Shehu ya ce sato jawabin ba laifin Buhari ba ne, inda ya dora laifin a kan mutumin da ke rubuta wa shugaban jawabi.

Ya kuma kara da cewa za a daukin matakan ladabtar da jami'in da ya rubuta jawabin.

Wani marubuci a jaridar ThisDay mai suna Adeola Akinremi ne ya fara tayar da maganar a wata makala da aka wallafa ranar Juma'a.Wani marubuci a jaridar ThisDay mai suna Adeola Akinremi ne ya fara tayar da maganar a wata makala da aka wallafa.

Jawabin Barack Obama

".......Lallai ne mu lizimci wata sabuwar dabi'a ta kishin kasa, da sanin ya-kamata, inda ko wannenmu zai kuduri aniyar ba da gudummawa....

"...Mu kuma kara aiki tukuru mu kula da junanmu ba kanmu kadai ba....

"Mu tuna cewa idan akwai wani abu da wannan matsalar tattalin arzikin ta koya mana shi ne ba zai yiwu a samu masu hannu da shuni suna fantamawa ba, yayin da marasa galihu ke cikin wahala."

Jawabin Buhari

"...Lallai ne mu lizimci wata sabuwar dabi'a ta sanin ya-kamata, dabi'a ta yi wa kasa hidima, da kishin kasa, da kuma sadaukar da kai....

"Lallai ne gaba dayanmu mu kudiri aniyar ba da gudummawa mu kuma yi aiki tukuru, mu kuma kula da junanmu ba kanmu kawai ba....

"Abin da matsalar da muke fama da ita yanzu ta koya mana shi ne ba zai yi wu ba wani gungun mutane cima-zaune su rika fantamawa yayin da galibin al'umma ke cikin wahala".