Shagon Dan Sama'ila ya kai wasan zagayen gaba a gasar damben gargajiya

Shagon Dan Sama'ila ya buge na Buhari
Bayanan hoto,

Shagon Dan Sama'ila ya buge na Buhari a damben gasa

Shagon Dan Sama'ila ya kai wasan zagayen gaba a gasar damben gargajiya da za a lashe mota a karawar da ya yi a ranar Talata a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

Shagon Dan Sama'ila dan damben Kudu ya yi nasar doke Shagon Shagon Buhari ne dan wasan Arewa a turmin farko.

Shi ma Shagon Shagon Dan Digiri daga kudu ya kai wasan zagayen gaba a gasar bayan da ya buge Bahagon Na Baciraw daga Arewa a turmin farko.

I zuwa yanzu 'yan dambe tara ne suka rage a gasar da suka hada da 'yan wasan kudu biyar a tsaye da 'yan Arewa biyu da kuma guda biyu daga Guramada.

Ali Kanin Bello daga Arewa zai dambata da Kurarin Kwarkwada daga Kudu a ranar Laraba, daga nan ne za a raba jadawalin wasannin daf da na kusa da karshe.