Abin da suturar Clinton da Trump ke nunawa game da su

Ba abubuwan da Hillary Clinton da Donald Trump su suka faɗa lokacin da suka gamu da juna a muhawarar su ta farko ake dubawa ba, har ma da irin shigar da suka yi
Bayanan hoto,

Ba abubuwan da Hillary Clinton da Donald Trump su suka faɗa lokacin da suka gamu da juna a muhawarar su ta farko ake dubawa ba, har ma da irin shigar da suka yi

Lokacin da Hillary Clinton ta hau kan dandamali a zauren muhawarar 'yan takarar shugaban kasar Amurka, ta kafa tarihi.

Domin cikin watanni da suka gabata an yi ta binciken ƙwa-ƙwaf akan ta, kasancewar ita ce mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin Amurka.

An dai yi ta sharhi akan manufofinta da sakonninta na emails, har ma da irin suturar da take sanyawa.

Babu inda ake fi sa ido a lokutan siyasa akan sutura da kuma gyara gashin mutum kamar Amurka.

Masu sharhi sun yi ta tsokaci akan farar rigar kwat da Clinton ta sanya a lokacin babban taron jam'iyyar Democrat, inda suka fassara shigar ta a matsayin haske maganin duhu.

Shi kuwa Donald Trump an yi ta tsokaci game da suturar da yake sanya wa har ta kaiga akan yi masa shaguɓe akan yanayin fuskar sa da kuma rigar kwat da yake sanya wa da kuma yadda yake gyara gashin kansa, kai har ma da yanayin girmar hannun sa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu sharhi sun yi ta tsokaci akan farar rigar kwat da Clinton ta sanya a babban taron jam'iyyar Democrat

Mai yiwuwa a riƙa kallon irin wannan yanayi a matsayin shirme musamman idan aka taɓo batun tafiyar da mulkin ƙasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Amma kuma zai kasance babban kuskure a riƙa fassara cewa yanayin shigar da mutum ke yi bai da tasiri a siyasa, domin kuwa gaskiyar magana, 'yan siyasar wannan zamani sun dogara ga abun da ake faɗa da kuma abun da ake gani a zahiri.

Kuma wannan ba sabon abu ba ne domin kuwa a shekarar 1960 lokacin da zaɓe ya kasance babbar al'amari ga gidajen talbiji, an bayyana cewa muhawarar da aka watsa ta talbijin tsakanin Nixon da Kennedy ita ta yi sanadiyyar nasarar Kennedy a zaɓen.

Kuma wasu sakamako na bincike sun tabbatar da cewa shigar dan takara yana da tasiri a siyasa fiye da yadda mu ke zato.

Domin wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyyar halayyar dan adam a shekarar 2006 da Alexander Todorov na jami'ar Princeton ya jagoranta, ya nuna cewa masu aikin sakai wadanda suka kalli hotunan 'yan takara na wani dan ƙanƙanen lokaci, za su iya hasashen wanda zai lashe zaɓen da kusan kashi 70 cikin 100 a zaɓen 'yan Majalisar dattawa data wakilai a 2006.

Kuma idan aka duba ta wannan ɓangaren, furucin da Marco Rubio ya yi game da yanayin hannun Trump bai tsaya ga yarfen siyasa ba kadai, wata hanya ce ta nuna rashin ƙwarewar Trump wajen iya shugabanci.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi ta tsokaci game da suturar da Donald Trump ke sa wa har ta kaiga akan yi masa shaguɓe game da fuskar sa da girmar hannun sa

Dr Rebecca Arnold, malama ce dake koyar da tarihin sutura a cibiyar Courtauld ta amince cewa sha'awar shigar da wasu 'yan siyasa ke yi tana ƙaruwa ne a wannan zamani da shafukan sada zumunta da muhawara su ka yaɗu.

" Wannan ya nuna irin al'adun mu baki daya - hankula sun fi matuƙar karkata akan yanayin shigar mutum da kuma yadda mutum ya gabatar da kansa, wadanda su ne ke karkata al'amurran kafofin sadarwa na zamani".

Sai dai Dr Arnold ta ƙara da cewa, tabbas an fi karkata ta ɓangaren jinsi.

"Ta ce an fi maida hankali akan mata saboda babu tsarin sutura iri ɗaya kamar kwat na maza, amma yana da muhimmanci a tuna cewa wannan ba ya tsaya ne ga mace 'yar siyasa ba kaɗai, saboda ana yawan sa matai do musu ido kuma ana yi musu mummunar fassara saboda da zaɓin da suka yi."

Dalilin hakan kuwa shi ne samun mace da ta samu shugabanci da ta zamo abun misali wani abu ne ya kasance da kamar wuya, a cewar Lauren A Rothman, mai gyaran gashi da ke zaune a birnin Washington DC- kuma wacce ta wallafa littafi kan yadda ake kwalliya mai suna: What To Wear To Work.

"Ta ce bamu da misali masu yawa na irin shigar da mata da suke shugabanci ke yi."

Saɓannin haka, ba'a cika duba irin shigar da maza ke yi ba.

"Ta ce ga maza, akwai irin suturar da ta zama gama gari wajen tafiyar da mulkin ƙasa, kwat mai ruwan shudi da farar riga da kuma laktai na launin ja ko kuma shudi.

Amma kuma har yanzu ba'a samu suturar data zama gama gari ga mata ba, kuma inda ganin zamu yi ta ganin tsarin sanya suturu na wasu mata da suka samu shugabanci da zasu riƙa fitowa".

Mace ta kasance ta farko

Bisa al'ada, matan da mazajensu ke shugabancin ƙasashe da kuma matan 'yan siyasa sun tari aradu da kai ta fuskar sanya kayan ado.

Angela Merkel ta ɗauki tsarin sanya kayan da ya zama gama gari wajen maza, inda ta yarda da irin tunanin da wasu ke yi cewa mace ta fi kwarjini idan ta riƙa yin shigar da maza ke yi.

Wannan wani yanayin ɗinki ne da Michelle Bachelet na ƙasar Chile, da kuma Dilma Rousseff na kasar Brazil har ma da Firai Ministan farko a Scotland Nicola Sturgeon suke yi.

Margaret Thatcher kuwa yanayin shigar ta daban yake, tana sanya suturar ta tare da ƙaramar jakar hannu yayin da tsohuwar shugabar Argentine Cristina Fernández de Kirchner aka santa da caɓa ado a dinkunan da akan yi da leshi.

A yanzu Hillary Clinton da Theresa May, mata biyu da suke kan mulki suna sauya yadda ya kamata matar da ke shugabanci a duniya ta riƙa yi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi ta la'akari da yadda Theresa May ke caɓa ado

Daga irin yadda take sha'awar caba ado da kuma irin 'yan kunne da sarƙar wuyar da take sanya, an yi la'akari da yadda Theresa May ke caɓa ado.

Firai Ministan ta nuna yadda take son kwalliya tare kuma da gudanar da aikin ta.

Wannan wata nasara ce ga ƙananan mata cewa za su iya sha'awar kwalliya kuma a ɓangare guda suna riƙe da muhimmin muƙami.

Sai dai kuma tana yin kwalliyar ta da dabara, saboda da zarar ta tsaya a gaban gidan Firai Minista sanye da rigar sanyi, hotunan ta ke cika shafukan internet tun ma kafin wani ya samu lokacin nazarin abun da ta ce.

Sabuwar Firai Ministan ta fahimci cewa sutura ita ce mutuncin mutum, kuma ga Theresa May, sha'awar ta wajen kwalliya ya ƙara mata ƙima.

Mai yiwuwa ra'ayin Clinton ba zai zo daya ba da May kan batun daya shafi sanya sutura, amma dai ta san muhimmancin sutura.

Dabi'ar ta game da kwalliya ya sauya tun bayan zaben shugaban ƙasar Amurka da aka gudanar a baya inda ta dauki hayar Kritina Schake, tsohuwar ma'aikaciyar Michelle Obama, don taimaka mata farfado da ƙimar ta tare da daukar wata da ta ƙware a harkar kwalliya.

Har ta fito a mujallar nan ta Amurka mai suna Vogue, mujallar da a baya can ta riƙa kaucewa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwalliya na daga cikin makamin da Clinton za ta iya amfani a yaƙin neman zabe

"A baya lokacin da ta fara tsayawa takara, abun da aka yi da shaidar ta akai shi ne tana shiga irin ta maza, a yanzu tan amfani da surar ta ta mace da kuma yanayin suturar ta wajen nuna cewa ita ce," kamar yadda Rothman ta bayyan.

"Koda tana nuna kanta a matsayin uwa ce ko kuma kaka ce abun da take cewa shine ni mace ce".

Wato za'a iya cewa kwalliya na daga cikin abubuwan da Clinton za ta iya amfani a yaƙin neman zabe

Ka yi da gaske?

Babbar hanyar da za'a duba yadda 'yan siyasa ke sanya sutura ba tare da la'akari da jinsi ba, shi ne duba aniyar su, ba kawai ko don ana yayin suturar ba kamar yadda Dr Arnold ke cewa.

Rothman aya amince cewa. "Duk wannan wani bangare ne na aikewa da sako, akwai wasu 'yan siyasa da suke dogaro da irin shigar da dan siyasa ke yi.

Wannan ya kawo mu ga Jeremy Corbyn, mutumin da wasu da dama suka yi ta sukar sa wadanda suka hada da mahaifiyar David Cameron saboda ya sabawa sanya siturar al'ummar sa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane da da dama sun yi ta sukar Jeremy Corbyn wadanda suka hada da mahaifiyar David Cameron

Donald Trump ya yi la'akari da haka kamar yadda Rothman ke cewa.

" Yana ƙokarin ya rika shigar da 'yan siyasa ke yi, bai sanya rigar da ta yi masa yawa. "Trump na zaben sutura ce kamar sauran 'yan siyasa maimakon wani nai sayen hannayen jari kuma wannan yasa ya kara samun magoya baya."

Tsarin kwat da nakitayi ya sha banban da irin shigar Barack Obama da kwat din sa ke kamar a matse kadan da rigar da ke cikin kwat din.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump bai taba sauya yanayin shigar sa ba a daukacin lokacin da yake yaƙin neman zabe

Tun ma kafin ya fara neman takarar shugaban ƙasa, Trump ya fahimci muhimmanci yanayin shigar mutum.

Mai yiwuwa za'a dade ana shagube akan yanayin gashin kan sa da kuma launin jikin sa, amma sun ƙarfafa Trump, da kuma abun da zai iya samu a zukatan masu kada ƙuri'a.

Yayin da ya kamata a riƙa yiwa 'yan takara kyakyawar fassara akan sakonnin da suke aikewa, a wannan ƙarni na yadda shigar mutum ne ke zama abun labara, zai zama shirme a kau da kai irin sakonnin da sura da shigar 'yan takarar ke aikewa.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: What Clinton and Trump's clothes tell us about them