Amurka: Majalisa ta soke damar Obama ta hana gurfanar da Saudiya

Obama ya ce an tafka babban kuskure
Bayanan hoto,

Shugaba Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce majalisar kasar ta tafka babban kuskure da ta soke damar da doka ta bashi wajen hana iyalen mutanen da harin 11 ga watan satumba ya rutsa da su kai gwamnatin Saudi Arabia kara.

Obama ya ce matakin majalisar ya kawar da ikirarin da ake na cewa kasashe suna da wata kariya, kuma hakan zai bada damar daukar matakin shari'a a kan dakarun Amurka ko kuma jami'an kasar da ke aiki a kasashen waje.

Shekaru 10 iyalen mutanen da harin ya rutsa da su suka shafe suna kokarin ganin sun samu wannan dama ta doka, kuma suna fatan hakan zai basu damar gabatar da korafin su a kotu wataran.

15 biyar daga mutane 19 da suka yi fashin jirgin da aka kai harin da shi cibiyar kasuwanci ta duniya dai 'yan Saudiya ne, kuma an jima ana zargin cewa kasar ta Saudiya ta bada kudi a asirce domin kai harin.

Gwamnatin ta Saudiya a ko yaushe tana musa cewa tana da hannu.

Ta kuma jima tana rokon kada a gurfanar da ita a kotu kan batun, har ma ta yi barazanar cewa idan aka matsa mata, zata janye kadarorinta na biliyoyin daloli daga Amurka.

To sai dai wadanda suka kada kauri'ar sun ce Shugaba Obama ya fi damuwa da huldar jakadanci, fiye da iyalen wadanda harin ya rutsa da su da kuma fafutukar samun adalci.