An gano yadda za a shawo kan HIV

AIDS ta kashe miliyoyin mutane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Binciken zai taimaka wajen shawo kan cutar

Wani bincike da masana kimiyya suka yi ya gano cewa kashi goma cikin dari na yaran da suka kamu da HIV ba sa kamuwa da AIDS ko da kuwa ba a yi musu magani ba.

Gwaje-gwajen da aka gudanar a kan yara 170 'yan kasar Afirka ta kudu da ke dauke da HIV ya gano cewa garkuwar jikinsu tana juyawa kamar ta halittun da suke da cutar a baya.

Masanan sun ce binciken zai iya zama wata alama ta farko da ke nuna cewa mutane za su iya rayuwa ko da suna dauke da HIV ba tare da wata matsala ba.

Sun kara da cewa binciken zai zama wata sabuwar hanya ta samar da magani ga masu dauke da kwayoyin cutar.