'Sudan ta jefawa kananan yara makamai masu guba a Darfur'

Gwamnati ta musanta zargin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaran da suka tsira daga harin suna korafin cewa idanunsu da fatarsu sun sauya kama

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Sudan da kashe yara da dama a yankin Darfur ta hanyar amfani da makamai masu guba a kansu.

Amnesty International ta ce yaran na cikin yara fiye da 200 da aka kiyasta cewa an kashe tun daga watan Janairu ta hanyar amfani da makaman masu guba wadanda kuma aka haramta amfani da su.

Rahoton kungiya ta ce yaran "sun shaki hayaki mai guba" inda suka rika yin aman jini da fama kan yadda za su yi numfashi a yayin da suna kallo fatar jikinsu tana konewa.

Sai dai gwamnatin Sudan ta musanta zargin, tana mai cewa ba shi da tushe bare makama.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya mabato Jakadan Sudan a majalisar dinkin duniya Omer Dahab Fadl Mohamed yana cewa "zargin ba shi da makama, kuma an kitsa rahoton ne kawai."

A cewarsa, an fitar da rahoton ne domin yin kafar-ungulu a yunkurin da kasar ke yi na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar.

Gwamnatin kasar da 'yan tawaye dai sun kwashe shekara 13 suna yaki a yankin na Darfur.

Sai dai kasashen duniya ba su mayar da hankali kan rikicin kasar ba.