Bai kamata a sayar da kaddarorin gwamnati ba — Obasanjo

Tsohon shugaban Nigeria Cif Olusegun Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Obasanjo ya yi kira da a yi garambawul ga kamfanonin gwamnati

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce bai kamata a sayar da kaddarorin gwamnati domin ceto kasar daga tabarbarewar tattalin arzikin da take ciki ba.

Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban babban kamfanin mai na kasar, NNPC, Maikanti Baru ya kai masa ziyara a gidansa da ke birnin Abeokuta ranar Laraba.

Wata sanarwa da kakakin NNPC Garba Deen Muhammad ya fitar, ta ambato Mista Obasanjo yana cewa, "ya kamata a yi sauye-sauye. Na yi amannar cewa ya kamata a yi wa kamfanoni irinsu NNPC garanbawul. Sayar da kaddarorin gwamnati bai dace ba".

Obasanjo ya kara da cewa idan aka yi wa NNPC garanbawul Najeriya za ta fita daga halin tabarbarewar tattalin arzikin da take ciki.

A kwanakin baya ne dai wasu manyan'yan siyasa da 'yan kasuwar kasar cikinsu har da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Aliko Dangote suka yi kira ga gwamnati ta sayar da kaddarorinta irinsu kamfanin mai da iskar gas, NLNG domin ta samu kudin da za ta gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

A ranar Laraba ne majalisar zartarwa ta Najeriya ta fara tattaunawa kan batun sayar da kadarorin, wanda ministan tsare-tsare ya gabatar mata.

Amma kawo yanzu ba ta cimma matsaya kan matakin da za ta dauka ba.

Sai dai wasu masana tattalin arziki da 'yan kasar sun nuna matukar adawa ga wadannan kiraye-kiraye.

Ita ma majalisar dattawan kasar ta yi da wannan shawara, sannan ta yi kira ga gwamnati da ta yi taka-tsan-tsan.