Zakarun Turai: Walcott ya ci Basel kwallaye biyu

Theo Walcott

Asalin hoton, Rex Features

Arsenal ta doke Basel da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka fafata a ranar Laraba a Emitares.

Theo Walcott ne ya ci kwallayen biyu, daya a minti na bakwai da fara wasa, ya kuma kara ta biyun a minti na 26.

Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na biyu a rukunin farko da maki hudu a wasanni biyu da ta buga a gasar.

Paris St Germain ce ke matsayi na daya itama da maki hudun, bayan da ta ci Ludogorets Razgrad 3-1 a karawar da suka yi a ranar Talata.

Arsenal za ta karbi bakuncin Ludogorets Razgrad a wasa na uku a cikin rukuni na ranar Laraba 19 ga watan Oktoba.