Zakaran Firimiyar Nigeria zai karbi naira miliyan 40

Sheu Dikko

A ranar Lahadi ake sa ran buga wasannin karshe a gasar Firimiyar Nigeria, inda zakaran bana zai karbi ladan kudi naira miliyan 40.

Shugaban gudanar da gasar Shehu Dikko ya ce kudin da zakaran zai samu jumulla zai kusan kai naira miliyan 100, idan aka hada da kudin da suka bai wa kungiyoyin tun fara gasar bana.

Dikko ya ce sukan raba kudi ga kungiyoyi 20 da suke buga wasannin kashi hudu, tun farkon gasar har zuwa karshenta.

Da farko suna raba kudi daidai ga kungiyoyin jumulla, da ladan cin wasa a waje ko yin canjaras ko 'yawan magoya baya da suka shiga kallon wasa da bai wa kulob din da ya saka 'yan wasa uku masu shekara 18 a wasa kudi.

A karshen gasar a kan raba kudi ga kungiyoyin daidai kokarinka shi ne yawan kudin da hukumar ke bai wa kulob.

Enugu Rangers ce ke mataki na daya a kan teburi ta kuma bai wa Rivers United wadda ke matsayi na biyu tazarar maki uku, Rangers din za ta buga wasan karshe da El Kanemi a gida, inda Rivers United za ta ziyarci Akwa United.

Haka kuma kungiyoyi hudu ne za su fado daga gasar bana, wadda tuni Giwa FC da Ikorodu United suka yi bana, saura kungiyoyi biyu ne da za su bi sahunsu.