Shugaban Colombia Juan Manuel Santos ya lashe kyautar Nobel

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da shugaban Farc

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akalla mutane 260,000 ne aka kashe a yakin da aka shafe shekaru 52 ana gwabzawa

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel duk da halin rudanin da yarjejeniyar da ya kulla da 'yan tawayen Farc ta shiga.

Alkalai a Norway sun yaba masa kan yarjejeniyar da ya kulla da Farc a watan jiya bayan shafe shekara hudu ana tattaunawa.

Sai dai al'ummar Colombia sun yi watsi da shirin a zaben raba-gardamar da aka gudanar a makon da ya gabata.

Akalla mutum 260,000 ne aka kashe a yakin da aka shafe shekara 52 ana gwabzawa a kasar.

Kazalika sama da mutum miliyan shida ne aka raba da gidajensu.