Bincike ya gano cewa magungunan kashe radadi na kara yiwuwar bugawar zuciya

Magungunan kashe radadin ciwo

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

Shan magungunan rage radaddin ciwo na da alaka da bugawar zuciya

Wani bincike ya gano cewar shan maganin kashe raɗaɗin yana da alaka da karin hadarin kamuwa da bugun zuciya.

Ana yawan amfani da magunguna da suke rage radadin ciwo ko kuma zazzabi , kamar su Ibuprofen da naproxen da diclofenac domin rage ciwo ko kuma kumburi.

Wata mujalla kan kiwon lafiya da ake bugawa a Birtaniya, ta British Medical Journal, ta yi bincike kan mutum miliyan 10, masu kimanin shekara 77, wadanda suke shan wadannan kwayoyin magani.

Masana a Birtaniyan sun ce sakamakon binciken ba shi da wai muhimmanci ga mutanen da shekaransu basu ka 65 ba, amma abin damuwa ne ga tsofaffi marasa lafiya.

Binciken ya yi nazari kan bayanai na mutum miliyan 10 da ke shan magungunan, wadanda 'yan kasar Birtaniyan da Netherlands da Italy da kuma kasar Jamus ne -- kuma aka kwatanta su da mutanen da ba su sha magungunan ba.

Masu bincike daga jami'ar Mialno-Bicocca da ke kasar Italiya sun gano cewar shan magungunan kashe radadin ciwo na kara yiwuwar hadarin kamuwa da ciwon zuciya da kashi 19 cikin 100.