Rikicin Kashmir: India ta kai hari kan iyakar ta da Pakistan

Sojan Indiya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

India ta kai hari kan iyakar ta da Pakistan

Sojojin India sun ce sun kai hari kan wasu wadanda ake zargin masu tada kayar baya ne a kan iyakarta da Pakistan a Kashmir.

Wani babban jami'i ya ce sun kai harin ne domin kare afkuwar wasu hare-hare da masu tada kayar bayan Pakistan suka shirya kai wa.

Ya ce "sun raunana masu tada kayar bayan da dama da ma masu kokarin taimaka musu".

Sai dai Pakistan din ta musanta cewar India ta kai mata hari, kuma ta ce an kashe sojojin ta biyu a barin wutar da aka yi tsakanin bangarorin guda biyu.

A wata sanarwa da sojin Pakistan ta fitar, ta ce "India ta na kai irin wadannan hare-hare ne domin ta ja hanakalin duniya.