Dan kwallon Arsenal, Aaron Ramsey, ba zai buga wa Wales wasa ba

Aaron Ramsey a fillin wasan kwallon kafa

Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Bayanan hoto,

Aaron Ramsey, ba zai buga wa Wales wasa ba

Dan kwallon Arsenal, Aaron Ramsey, ba zai buga wa Wales karawar da za ta yi da Austria da Georgia ba a watan gobe.

Ramsey ya yi rauni ne a wasan da Arsenal ta doke Chelsea 3-0 a gasar cin kofin Premier a ranar Asabar.

Haka shima Jonny Williams ba zai buga wasannin ba sakamako jinya da yake yi.

Sai dai Gareth Bale mai taka leda a Real Madrid yana cikin jerin 'yan wasan da za su buga wa Wales wasannin.

Wales za ta kara da kasashen biyu a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.