Gareth Southgate ya ce abu ne mai mahimmaci ka haror da Ingila

Gareth Southgate ne mai horar da Ingila na rikon kwarya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gareth Southgate, martaba ce ka horar da Ingila

Gareth Southgate ya ce abu ne mai mahimmaci ka jagoranci tawagar kwallon kafa ta Ingila.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ce ta bai wa Southgate aikin horar da kasar na rikon kwarya, bayan da ta taba gari da Sam Allardyce.

Southgate wanda ke horar da matasan Ingila masu shekara 21 zai ja ragamar babbar tawagar kasar wasanni

Allardyce da Ingila sun raba gari ne a ranar Talata, bayan wani bincike da wata jarida ta gudanar, wadda ta ce kiciyan ya bayar da shawara kan yadda za a karya ka'idar sayen 'yan kwallon.

A cikin watan Yuni Southgate ya ce bashi da niyyar karbar aikin horar da Ingila, domin maye gurbin Roy Hodgson wanda ya yi ritaya.

Haka kuma kociyan Arsenal Arsene Wenger dana Bournemouth Eddie Howe da ake dangantawa da karbar aikin sunce hankalinau na kan kungiyoyin da suke jagoranta.