Najeriya ba za ta rage man da take hakowa ba
An kebe Nigeria daga yarjejeniyar Opec
Babban magatakardan kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta Opec, ya ce Nigeria ba za ta rage yawan man da take hakowa ba yanzu saboda wani yanayi na musamman da kasar ta shiga.
Dakta Muhammad Sanusi Barkindo ya shaida wa BBC cewa an kebe Najeriya da Iran da Libya a yarjejeniyar rage adadin man da kasashen ke fitarwa, saboda ba sa samar da yawan man da ya kamata ace suna samarwa.
Mista Barkindo ya ce " idan aka ce su rage, to ba a yi musu adalci ba".
A ranar Laraba ne kasashen da ke cikin kungiyar ta OPEC suka amince su rage yawan man da suke hakowa, bayan taron da suka yi a kasar Aljeriya.
Naziru Mikailu ya tattauna da Dakta Barkindo domin jin karin bayani kan yarjejeniyar da aka cimma: