Kanin Bello ya kai wasan daf da karshe a damben mota

Ali Kanin Bello dan damben Arewa
Ali Kanin Bello ya kai wasan daf da karshe a gasar damben mota da ake yi a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.
Kanin Bellon dan damben Arewa ya kai zagayen gaba ne, bayan da ya buge Dan Ali daga Kudu a turmin farko a ranar Alhamis.
Shima Shagon Audu Tunga Guramada ya kai wasan daf da karshe bayan da ya doke Shagon Dan Digiri daga Kudu a turmi na uku.
Za a ci gaba da wasannin daf da na kusa da na karshe tsakanin Sojan Jango Guramada da Kada daga Kudu, sannan a kece raini tsakanin Bahagon Sanin Kurna da Shagon Sama'ila a ranar Juma'a.