Legia za ta kara da Madrid ba ‘yan kallo

Asalin hoton, Getty Images
An hana 'yan kallo shiga wasan sabo da gudun hatsaniya
Kungiyar Legia Warsaw za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai ba tare da magoya bayanta ba.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta yanke, bayan da magoya bayan kungiyar suka tayar da hatsaniya.
Mogoya bayan Legia sun tayar da rikici a karawar da Borussia Dortmund ta casa kungiyarsu 6-0 a wasan farko na cikin rukuni da suka yi a gasar.
Haka kuma hukumar ta ci tarar Legia kudi fam 69,000.
Warsaw za ta karbi bakuncin Madrid a wasa na uku a cikin rukuni a ranar 2 ga watan Nuwamba.