Man United ta doke Zorya 1-0

Ibrahimovich ne ya ci kwallon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Man U ta doke Zorya

Manchester United ta ci Zorya Luhansk daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa da suka kara a ranar Alhamis.

Ibrahimovich ne ya ci kwallon bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon United ta koma mataki na uku a kan teburin rukunin farko da maki uku a wasanni biyu da ta yi.

Feyenoord ce ke matsayi na biyu ita ma da maki ukun, inda Fernabahce ke jagorantar rukunin da maki hudu.

A ranar 20 ga watan Oktoba United za ta karbi bakuncin Fernabahce a wasa na uku a cikin rukuni a gasar ta Europa.