Rooney zai ci gaba da zama kyaftin din Ingila

Rooney zai ci gaba da zama kyaftin Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rooney zai ci gaba da zama kyaftin Ingila

Kociyan rikon kwarya na tawagar kwallon kafa ta Ingila, Gareth Southgate, ya ce Wayne Rooney ne zai ci gaba da zama kyaftin din kasar.

Southgate wanda ya karbi aikin jan ragamar Ingila a ranar Talata, ya tattauna da Rooney a ranar Alhamis.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ce ta nada Southgate kociyan rikon kwaryar tawagar, bayan da ta raba gari da Sam Allardyce.

Southgate zai bayyana sunayen 'yan wasan da za su wakilci Ingila a ranar Lahadi domin fuskantar Malta da Slovenia a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.