Yunkurin hana matasan Africa zuwa turai don ci-rani

Ana so a hana matasan Africa kwarara turai ba bisa ka'ida ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Africa na gamuwa da hadura yayin tafiyar

An kaddamar da wani gangami na yaki da dabi`ar `yan Afirka ta kwarara kasashen Turai da sunan ci-rani ko kaura ba bisa ka`ida ba.

Gangamin wanda aka kaddamar a Najeriya zai maida hankali ne wajen wayar da kan al`umar nahiyar Afirka, musamman matasa a kan hadarin da ke tattare da yin balaguron, da kuma matakan da ya kamata gwamnatoci su dauka don magance matsalar, maimakon dogaro da kasashen Turai.

Dan majalisar dattatawan kasar mai rajin kare hakkin bil`adama, Sanata Shehu Sani ne ya kaddamar da gangamin a Abuja.

Sanata Shehu ya ce yunkurin zai taimaka wajen hana samari da 'yan mata a suke tafiya turai da su gujewa tafiyr mai hadari, maimakon haka su tsaya a gida su koyi sana'a don dogaro da kai.

Yace za a iya cimma wannan buri ta hanyar wayar da kan mutane, da kuma matsawa gwamnatoci lamba su taimakawa matasan da hanyoyin dogaro da kai.