Ban kullaci kowa ba - Hindatu Umar

Ta ce ba ta kullaci masu sukar ta ba.
Bayanan hoto,

Hindatu Umar ta ce za ta fi maida hankali wajen ilimi

Matashiyar nan da aka nada shugabar karamar hukumar Argungu a Jihar Kebbi Hindatu Umar ta ce ba ta kullaci kowa ba, duk kuwa da sukar nada ta da jama'ar jihar da dama ke yi.

Nadin na ta ya janyo ce-ce ku-ce, wasu na maraba, wasu kuma suna suka.

"ni ba ni da abokin adawa, a matsayina na mai jagorantar karamar hukuma kowa masoyi na ne, sannan ya kamata su gane Allah ya kawo mana chanji. Lokaci ya ya na chanji. Muma matasa ana yi da mu, mu godewa Allah ba mu yi fada ba." Inji Hindatu

Hindatu ta shedawa BBC cewa ba ta taba tunanin kaiwa irin wannan matsayi ba.

Tace a da fatanta shi ne ta zama malamar makaranta, to amma kuma sai ta tsinci kanta a bangaren shugabanci.

Hindatu ta ce za ta fi maida hankali kan ilimi da sana'a, da noma.

Ita ce mace ta farko da ta zama shhugabar karamar hukuma a jihar ta Kebbi

Ba kasafai ake nada mata irin wadannan matsayi ba.