Amukar da Rasha na cacar baki kan rikicin Syria

Kasashen sun samu sabani kan yakin da ake yi a Syria
Bayanan hoto,

John Kerrey na Amurka da Sargey Labvrov na Rasha

Hukumomin Amurka sun ce suna daf da dakatar da duk wata huldar diplomasiyya da Rasha kan batun Syria, gami kuma da neman wata hanyar tunkarar yakin basasar da ake a Syria.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace babu hikima a ce za a dauki matakan diplomasiyya da mahimmanci, ganin irin ruwan wutar da ake yi a birnin Alepo.

Ya ce matakin da Rasha ke dauke ya fara wuce makadi da rawa, kuma matukar tura ta kai bango, Amurka za ta san matakin da za ta dauka.

A nata bangaren Rasha watsi ta yi da kiran da Amurka ta yi mata, inda ta ce babu abinda zai dakatar da ita da ga kai hare hare kan 'yan tawayen na Syria a gabashin birnin Halab (Alepo).

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha Dmitry Peskov, ya ce sojojin sama na Rasha za su ci gaba da taimakawa dakarun Syria.

Ya kuma yi kira ga Amurka ta cika alkawarin da ta yi na cewa za ta raba tsakanin 'yan adawar Bassharul Assad masu sassaucin ra'ayi da kuma 'yan ta'adda.

Kasashen Rasha da Amurka sun shafe watanni suna tattanawa domin neman dakatar da yakin da ake yi a Syria, sai dai yarjejeniyar da aka cimma a baya bayannan ta rushe a makon jiya, bayan 'yan kwanaki da fara aiki da ita, kuma tun daga nan aka ci gaba da kai hare-hare a gabashin birnin Halab.