Boko Haram: Amurka za ta aike da jirage marasa matuka Nijar

Amurka ta sha alwashin kawar da 'yan ta'adda
Bayanan hoto,

Za a kafa sansanin a jihar Agadez

Gwamnatin Amurka ta kashe kimanin $50m domin kafa sansanin sojinta a Jamhuriyar Nijar.

Sansanin, wanda zai kasance a birnin Agadez, zai bai wa Amurka damar yin amfani da jiragenta marasa matuka domin kai hare-hare kan kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Boko Haram a kasashen Najeriya da Libya da kuma Mali.

Da ma dai Amurka tana da wasu sojoji a birnin Niamey, inda ita da Faransa ke amfani da wani sansanin sojojin sama domin kai hare-hare kan 'yan ta'adda.

An jibge jirage marasa matuka samufurin MQ-9 Reaper a can.

Wata mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka, Michelle Baldanza, ta tabbatar cewa kasarta ta amince ta biya kudade domin gina titin jirgi da wasu kayayyaki a Nijar.

Ta ce kudin da za a kashe ya kai $50m sai dai jaridar The Intercept, wacce ta fara wallafa wannan labari, ta ce kudin da za a kashe ya kusa ninka wanda Michelle Baldanza ta fada.

Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen yankin tafkin Chadi dai sun hada gwiwa domin fatattakar kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane, kana ta raba miliyoyin mutane daga gidajensu.