Rahama Sadau ta fara fitowa a waka salon hip hop

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Batun ya janyo ce-ce-ku-ce
Bayanan hoto,

Rahama ta yi fice a fina-finan Kannywood

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta fara fitowa a waƙa salon hip hop a karon farko tun da ta shiga harkar fim.

Jarumar ta fito ne a cikin wata waka da mawakin nan Classiq ya rera mai suna I Love You, wacce ke da tsawon minti hudu da dakika 19.

A cikin wakar dai an nuno jarumar a wurare da dama a kwance a jikin Classiq, wasu lokutan kuma sun rike hannayen juna, inda suke nuna shauƙi irin na "masoya".

BBC ta nemi jin ta bakinta kan dalilin da ya sa ta soma fitowa a wakoki irin wadannan, sai dai bata ba mu amsa ba.

Bayanan hoto,

Rahama Sadau da Classiq sun nuna shaukin sosayya a wakar

Rahama dai ta yi suna sosai wajen fitowa a fina-finan Kannywood, kodayake a bara ne ta fara fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

Ta shaida wa BBC cewa ta fara fitowa a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna bajintarta, tana mai cewa ba za ta yi duk wani abu da zai zubar mata da mutunci ba.

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba

Mabiyanta da ma masu sharhi a kan harkokin fina-finai sun bayyana mabambanta ra'ayoyi kan yadda aka ganta a wakar Classiq suna rungumar juna.

Wasu sun ce ta burge su da ta fara waka, yayin da wasu suka caccake ta suna masu cewa abin da ta yi ya sabawa tarbiyyar Hausawa.

Akwai jaruman Kannywood da suka yi fice a waka irinsu Adam A Zango da Sani Danja da kuma Yakubu Mohammed.

Bayanan hoto,

Rahama Sadau tana matukar sha'awar fina-finan Bollywood

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da ta fito a wakar turanci