'Yan Afirka sun taka rawa a rayuwata — Wenger

Wenger ya kwashe shekara 20 a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wenger ya ce 'yan wasan Afirka sun iya murza leda

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya shaida wa BBC cewa 'yan wasansa da suka fito daga nahiyar Afirka sun yi tasiri sosai a rayuwarsa ta kwallon kafa ta fiye da shekara 20.

Wenger na magana ne a wani taron manema labarai inda Arsenal ta hada masa liyafar ban-girma saboda ya kwashe shekara 20 yana kocinta.

Wenger ya kara da cewa 'yan wasan Afirka gwaraza ne masu hikima da zalaka da kuma iya murza leda ko da a cikin mawuyacin hali.

Ya ce 'yan wasa irinsu Nwako Kanu, Kolo Toure da George Weah sun yi tasiri sosai a rayuwarsa.