Juan Mata ba zai buga wa Spain wasa ba

Juan Mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Juan Mata bai buga Euro 2016 ba sai daga baya

Spain ta cire dan wasan Manchester United Juan Mata daga cikin 'yan kwallon da za su taka mata leda a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za su yi da Italiya da Albania a watan Oktoba.

An cire Mata, mai shekara 28, daga cikin tawagar da ta buga Euro 2016 kodayake daga baya sabon kocin Spain Julen Lopetegui ya sanya shi a cikin tawagar.

Kazalika Mata ya yi zaman benchi a wasan sada zumuci da Spain ta doke Belgium da ci 2-0 da ma wasan neman cancanta shiga gasar cin kofin duniya da suka doke Liechtenstein da ci 8-0 a watan da muke ciki.

Shhi ma dan wasan tsakiya na Chelsea Cesc Fabregas, mai shekara 29, ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wasan.

Ba a sanya shi a jeren 'yan wasan farko na tawagar ba.

Shi ma golan West Ham Adrian bai samu shiga cikin tawagar da za ta yi wasan ba.

Wasu daga cikin 'yan wasan da ke cikin tawagar su ne Diego Costa da David de Gea da David Silva da Nolito.

Spain, wacce ta doke Liechtenstein da ci 8-1 a wasansu na farko na rukunin G, za ta fafata da Italiya a Turin ranar 6 ga watan Oktoba sannan ta kara da Albania a Shkoder ranar tara ga watan na Oktoba.

Ga jerin sunayen 'yan wasan

David de Gea (Manchester United), Pepe Reina (Napoli), Sergio Rico (Sevilla).

Nacho Fernandez (Real Madrid), Jordi Alba (Barcelona), Dani Carvajal (Real Madrid), Sergio Ramos (Real Madrid), Gerard Pique (Barcelona), Javi Martinez (Bayern Munich).

Koke (Atletico Madrid), Sergi Roberto (Barcelona), Saul Niguez (Atletico Madrid), Sergio Busquets (Barcelona), David Silva (Manchester City), Lucas Vazquez (Real Madrid), Thiago Alcantara (Bayern Munich), Andres Iniesta (Barcelona), Isco (Real Madrid).

Jose Callejon (Napoli), Vitolo (Sevilla), Alvaro Morata (Real Madrid), Diego Costa (Chelsea), Nolito (Manchester City).