'Matan Nigeria sun fi na ko'ina mutuwa wajen haihuwa'

Matan Najeriya na mutuwa wajen haihuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An bukaci mata su rika yin tazara wajen haihuwa

Hukumar kula da yaduwar al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya, UNFPA, ta ce kashi goma cikin dari na mace-macen mata wajen haihuwa a duniya na faruwa ne a Najeriya duk da cewa al'ummar kasar kashi biyu ne kacal cikin dari na al'ummar duniya.

Shugaban hukumar Farfesa Babatunde Osetimehin ne ya fadi hakan a babban birnin kasar Abuja a karshen wata ziyara da ya kai kasar.

Farfesa Osetimehin ya ce bincike ya nuna cewa mata tsakanin 100 da 120 ne ke rasa rayukansu a kullum a kasar wajen haihuwa.

Ya kuma ce daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen faruwar haka har da rashin rungumar tsarin tazarar haihuwa.

A cewarsa, amfani da tsarin na tazarar haihuwa ka iya rage yawan mutuwar mata a wajen haihuwa da kashi talatin cikin dari.