Sojoji sun hana dubban fararen hula ficewa daga garin Yei a Sudan ta Kudu

Mutanen garin Yei a Sudan ta Kudu

Asalin hoton, UNHCR

Bayanan hoto,

Hukumar UNHCR ta nuna matukar damuwa kan mutanen da ke garin Yei

Hukumar da ke sa ido kan 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 100,000 ne suka kasa ficewa daga garin Yei da ke Sudan ta Kudu.

Kakakin hukumar, William Spindler, ya ce sojojin gwamnati na hana mutane fita daga garin ne bisa zargin cewa magoya bayan hambararren mataimakin shugaban kasar, Riek Machar, ne.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa maza da mata a cikin wani yanayi na kaduwa sun bayyana irin tashin hankalin da fareren hula ke fuskanta a can.

Haka kuma ta kara da cewa an kashe mutane, ciki har da mata da kananan yara, ta hanyar daddatsa su.

Sanarwar ta kuma ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, yayin da kayan amfanin gona ke lalacewa.

Bugu da kari mazauna garin na fuskantar hadarin cewa badi ba za su yi noma ba.