An haramta nuna fina-finan India a Pakistan

Asalin hoton, AP
Ba wannan ne karon farko da dangataka ke yin tsami tsakanin kasashen biyu ba
Manya-manyan gidajen sinima a kasar Pakistan sun hana nuna fina-finan India a wani mataki na nuna goyon baya ga dakarun sojin kasarsu.
An sanar da haramta nuna fina-finan ne a biranen Lahore da Karachi da kuma Islamabad.
Sun dauki matakin ne bayan dakarun sojin kasashen biyu sun soma tayar da jijiyoyin wuya a kan iyakar Kashmir.
A ranar Alhamis, kungiyar masu shirya fina-finan India ta Indian Motion Picture Producers Association, ta hana jaruman kasar Pakistan taka rawa a Bollywood.
Wani babban dan siyasar India mai ra'ayin kishin kasa ya umarci jaruman Pakistan da su fice daga kasar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin dakarun sojin kasashen biyu ke shafar sauran al'amuransu ba.