Me ya sa kuikuiyo ya fi babban kare masifa?

Galibi mu kan yi tunanin cewa kuikuiyon karnuka sun fi manyan karnuka kuzari da masifa, amma anya akwai hujjoji da ke nuna hakan?
Bayanan hoto,

Galibi mu kan yi tunanin cewa kuikuiyon karnuka sun fi manyan karnuka kuzari da masifa, amma anya akwai hujjoji da ke nuna hakan?

A duk lokacin da ka fita domin ka miƙe ƙafa a wuraren shaƙatawa, zaka riƙa ganin masu karnuka su yi nan su yi can riƙe da igiyar da suka ɗaure karnukan su.

A wasu lokutan ma kana iya kaciɓis da wani jibgegen kare amma kuma wani kuikuiyo yana ta yi masa haushi.

Mai yiwuwa ka taɓa ganin faifen bidiyo mai ban dariya na wani jibgegen kare na sheƙa gudu saboda masifar wani kuikuiyo.

Mun tambayi wasu jama'a ko suna zaton 'yan kuikuiyo sun fi manyan karnuka masifa?

Priyanka Habib ta bada amsa kai tsaye. " Ta ce kuikuiyo ya fi haushi da kuma masifa!"

Tawagar ta gano cewa wasu mutane waɗanda ke da ƙaramin jiki "sun fi saurin ɗaukar ɗumi" fiye da mutane masu ƙiba.

Alan Clark ya bayyana dalilan hakan:

"Ya ce ina ganin kuikuiyo da dama na fama da wata matsala da za'a ce ta ta'allaƙa ga ƙananan karnuka, saboda a duk lokacin da kuikuiyo na ya tunkari wani jibgegen kare abun bai da kyau."

Abu ne mai sauƙi mutum ya yi zaton cewa ko me yasa kuikuiyo ke da yawan faɗa.

Kamar yadda Travis Sounders ya ce, ba dole ne ba su kasance yadda ake kallon su, amma dai haƙiƙa galibi a shirye su ke su kare kan su.

Ya ya zaka ji idan aka ce kai ɗan mi-tsi-tsi ne?"

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Masu iya magana kan ce " fankan-fankan ba shine kilishi ba"

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

David Sandberg na jami'ar Buffalo dake New York da kuma Linda Voss na cibiyar kiwon lafiya wato Peninsula Medical School da ke Plymouth, a Burtaniya sun yi bitar hujjojin da binciken Napoleon ya gano da aka wallafa a shekarar 2002.

A ƙarshe sun amince cewa; "ɗabi'un da mutanen da su ke da ƙaramin siffa, galibi ba shi da bambanci ko a lokacin da su ke kanana ko suka zama samari, ko kuma idan suka manyanta."

Mu kan ga irin wannan yanayi a wasu lokuta.

Ba sabon abu ba ne yadda ake ganin dan mi-tsi-tsin tsuntsu na korar mikiya, amma kuma ba lallai ba ne yadda abubuwa su ke ga bil'adama su kasance ga dabbabobi.

Sakamakon wani bincike da aka wallafa a shekarar 2012, masu bincike ƙarkashin jagorancin P. Andreas Svensson na jami'ar Linnaeus dake Sweden sun gano yadda ɗabi'ar halittun kifayen da ake kira desert gobies.

Mazajen kifayen su ne ke kare sauran kifayen na desert gobies, a don haka sai masu binciken suka sanya wani nau'in kifi namiji a cikin su, kuma da ƙarfin tsiya mazajen kifayen desert gobies ɗin suka fatattaki wanda aka sanya a cikin su.

Masanan sun gano cewa ƙananan kifaye maza sun fi saurin kai farmaki fiye da manyan kifayen maza.

A don haka idan waɗannan ƙananan kifayen desert gobies za su yi irin wannan masifa, ko haka lamarin ya ke ga ƙananan karnuka?

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Me ya sa kuikuiyon karnuka su ka fi manyan karnuka masifa?

Paul Durnion ya ce: "Mun saba ganin yadda ɗan mi-tsi-tsin dabba ke korar wata babbar dabba, kamar dai yadda mu ke ganin ɗan mi-tsi-tsin tsuntsu na korar mikiya.

Chunyang Li ya bada shawarar cewa: " Mai yiwuwa kuikuiyo na jin tsoron manyan karnuka ne, saboda haka kowane lokaci kuikuiyo kan yi ƙokari kare kansa wanda ke nuna dabi'ar halittu masu ƙananan siffa."

Matsalar kuikuiyo na daga fargabar da masu karnukan ke da ita akan su.

A ƙasidar daya gabatar a 2013, Paul McGreevy na jami'ar Sydney dake Australia tare da tawagarsa sun yi bincike akan ko yanayin halittar karnuka na da alaƙa da dabi'un su.

Karnuka dai dabbobi ne da ake sha'awar su, a cewar McGreevy, "saboda ƙashin ƙwaƙwalwar su da kuma surar jikinsu sun bambanta daga wannan kare zuwa wancan".

Tawagar ta yi ƙokarin gano ko karnukan da ke da siffa iri daya halayyar su kan zo iri ɗaya.

Sun dai gano cewa kuikuiyo sun fi jin haushin masu karnukan su saboda yadda har sai sun roƙi a ba su abinci ko kuma idan za su yi fitsari ko kuma rashin maida hankali a kan su".

Wato dai bisa la'akari da wannan binciken guda,kuikuiyo sun fi manyan karnuka masifa, aƙalla a wasu lokuta.

Amma kuma sakamakon binciken bai fayyace mana ko me ya janyo haka ba.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Wani kuikuiyo na wasa da wani babban kare mai suna Jack Russell

Masu bincike sun amince cewa, ba zai taba yiwuwa ba a tantance sahihancin wannan sakamako tsakanin dangantakar kuikuiyo da manyan karnuka, domin yanayin girmar halitta na iya yin tasiri amma kuma hakan ba ya na nufin kowane kuikuiyo masifaffe ne ba.

Yana iya kasancewa kuikuiyo suna da wani abu a jikin su dake sa su yawan faɗa, amma kuma akwai wasu abubuwa da dama dake bukatar bayani- domin akasari hakan ya danganta ne ga yadda dan adam ke tafiyar da karnuka.

" Matsalar kuikuiyo tana daga fargabar da masu karnukan ke da ita gare su," in ji Emmet Folens.

"kuikuiyo na ganin cewa kasancewar su ƙanana, sun fi fuskartar hadarin wajen ji musu rauni daga manyan karnuka, haka kuma ba su cika barin su suna mu'amala tare ba."

Maimakon hakan, Hayley Bayles na ganin cewa "masu kuikuiyo su kan shagwaɓa su ta hanyar nuna musu tamkar su jarirai ne ba karnuka ba."

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Wani kuikuiyo a ƙaramar jaka

Abun da kawai sakamakon binciken McGreevy ya nuna shi ne dangantaka tsakanin girman jiki da kuma masifa, amma babu wata alaƙa a zahiri, a cewar Daniel Mills wani masanin halayyar dabbobi a jami'ar Lincoln dake Burtaniya.

" Ya ce yanayin girman jiki na yin tasiri amma hakan ba yana nufin kowane kuikuiyo masifaffe ba ne,".

Haka kuma ba mu da bayani akan ko wani irin kare ne ya fi wani zama masifaffe.

A gaskiya dai babu wata shaida da ta nuna cewa kuikuiyo sun fi jibga-jibgan karnuka masifa, amma watakila mutane su ke kawo irin wannan bambanci game da ɗabi'un karnukan, mai yiwuwa yanayin da suke kiwon kuikuiyo ya sha bambam da sauran ko kuma rashin fahimtar halayyar su.

Idan kana son karanta cikakken labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Why small dogs might really be more aggressive than big ones