Cacar-baka ta barke tsakanin Amurka da Rasha

Asalin hoton, Reuters
Rasha ta ce Amurka na goyon bayan 'yan ta'adda a Syria
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mark Toner, ya bayyana kalaman Mosko da ta ce Amurka na goyon bayan 'yan tawayen Syria masu alaka da Al Qaeda, a fakaice da cewa soki-burutsu ne.
Tun da farko dai ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya sheda wa BBC cewa Amurkawa sun kasa rarrabewa tsakanin 'yan tawaye masu matsakaicin ra'ayi da kungiyar masu ikirarin jihadi wadanda a da ake kiransu Nusra Front.
Bambancewa tsakanin mayakan 'yan tawayen Syria da ake kira masu matsakaicin ra'ayi daga kungiyoyin masu ikirarin Jihadi kamar su al-Nusra na daga wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Moscow da Washington a farkon watan Satumba.
Washington ta yi barazanar katse tattaunawar diflomasiyya da Rasha, idan Rashan da gwamnatin Syria ba su dakatar da ruwan bamabaman da suke yi wa birnin Aleppo ba.