Me ya sa Obama ke jan hankalin masu shirya fina-finai?

Wadanda suka fito a matsayin Obama da Michelle

Asalin hoton, Soda pictures

Bayanan hoto,

Yadda Obama ya fara soyayya da Michelle

Yayin da Barack Obama ya kusa kaiwa karshen wa'adinsa a fadar gwamnatin Amurka ta White House, masu shirya fina-finai suna mayar da hankulansu a kan farkon rayuwarsa.

An dai shirya wasu fina-finai biyu - Barry da Southside With You don nunawa a sinima. Ko mene ne dalilin da ya sa kuriciyar shugaban na Amurka ke jan hankulan masu shirya fina-finai?

Jaruman fina-finai na Hollywood, Parker Sawyers da Devon Terrel sun hadu ne kwanan baya a wajen wani taron liyafar bayar da lambar yabo ga fitattun 'yan wasan Hollywood ta Emmys a Los Angeles.

Jaruman biyu ba su taba haduwa ba, amma nan da nan suka shaida juna. Baya ga kasancewar dukkansu kamfani daya ke wakiltar su, ko wannensu ya fito a matsayin Obama lokacin yana saurayi a fina-finai daban-daban a bana.

A wata hira da aka yi da shi a kan rawar da ya taka a fim din Southside With You, Sawyers ya ce "Mutumin kirki ne, kuma mun yi hira sosai da shi".

Wasan kwaikwayo na soyayya da Richard Tannes ya shirya, wanda aka fitar a Amurka a karshen watan Agusta, wani wasan kwaikwayo ne a kan haduwar Barack da Michelle Obama ta farko a Chicago a shekarar 1989.

An yi cinikin kusan dala miliyan shida da dubu dari uku bayan nuna wasan a karo na farko a Burtaniya a wannan makon.

A fim din, Sawyers, wanda ya fito a matsayin Obama, ya yi kokarin ya jawo hankiln Michelle Robinson domin ta so shi a yini guda.

Sun halarci wani taron baje kolin zane-zane, sannan daga baya suka halarci wani taron al'umma suka kuma kare yinin da kallon fim din Do the Right Thing na Spike Lee a sinima.

Asalin hoton, Soda pictures

Bayanan hoto,

Hollywood ce ta shirya fim din soayyar Obama da Michelle

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sawyers, mai shekara 33, ya kusa ya rasa damar yin fim din saboda faifan bidiyo na farko da ya turo na gwajin bajintarsa, ya kwaikwayi Obama lokacin yana shekara 50.

Bayan watanni, bayan Tanne ya ba shi shawarwari, sai ya rage kwaikwayon, ya sake tura wani faifan bidiyon ya kuma yi nasarar samun damar.

Sawyers wanda ya girma a Indianapolis, amma yanzu yana zama a Ingila tare da iyanlinshi, ya fara fim ne a shekara 5 da suka gabata kuma ya samu fitowa a matsayin Obama a matsayin wani muhimmin mataki.

Daraktar fina-finai, Kathryn Bigelow ce ta fara shaida masa cewar yana kama da shugaban kasar Amurkan a lokacin da suke shirya fim din Zero Dark Thirty, wanda bai taka wani muhimmiyar rawa a ciki ba.

Ya kan kwaikwayi Obama a lokutan da suke shirya fina-finai domin ya nishadantar da abokan aikinshi.

Ya ce " A ko da yaushe ina jin cewar zan samu damar kwaikwayon shi a fim din tarihinshi, amma ban yi tunanin zan kwaikwaye shi a matsayin dan shekara 28 ba.

A iya sannin Sawyers, Obama da iyalinshi basu kalli fim din ba, amma yana dakin ajiyar kayan nishadi a fadar White House.

Shahararren mawaki, John Legend, wanda daya ne daga cikin wadanda suka hada fim din, ya ce ya gaya wa shugaban ya kalla.

Ko me yasa mutane za su so su kalli fim a kan haduwar Obama ta farko da matarsa?

" Mutane ne masu bada sha'awa kuma mutane suna mamakin yadda mutanen biyu, wadanda muke gani a talbijin suka hadu, " a cewar Sawyers.

Asalin hoton, Elevation pictures

Bayanan hoto,

Davon Terrell wani wanda ya taba zama Obama a fim din Barry

Ina ga babu wata tattaunawar da aka yi da shugaban ko matarsa da ake zurfafawa. Ba za ka iya tambayar wanne ne sumbatar da ka yi na farko? Ba zai da ce ba. " Don haka yanzu, muna hasashen yadda suka hadu ne kawai."

Sawyers yana fatan ya hadu da Obama wata rana. Mai zai ce idan ya hadu da shi?

A gani na zai ce nagode da ka yi wannan aikin. Na yi farin ciki da ya sadaukar da rayuwarsa domin yi wa jama'a aiki saboda abu ne da ya dace a yi.