Dambe ya halaka dan Burtaniya

Dambe ya halaka dan Burtaniya

Asalin hoton, SNS

Bayanan hoto,

Sau biyu abokin karawar Mike Towell yana kai shi kasa.

Wani dan damben boksin na Burtaniya ya mutu bayan an jikkata shi a wani dambe a birnin Glasgow na Scotland ranar Alhamis.

Sau biyu abokin karawar Mike Towell, mai shekara 25 wanda ya fito daga Dundee a Scotland, Dale Evans dan Wales yana kai shi kasa, kafin alkalin wasa ya dakatar da damben a turmi na biyar.

An bai wa Evans, taimakon gaggawa kafin daga bisani a garzaya da shi asibiti inda a can ya mutu.

Kafin wannan karawar ba a taba yin nasara a kansa ba a duk damben da ya yi guda 12.

Kwararrun 'yan damben Burtaniya hudu ne suka mutu sakamakon raunin da aka ji musu a yayin karawa daga 1986 zuwa yanzu.

Kafin Mike Towell, dan damben Burtaniya na karshe da ya mutu a sakamakon damben shi ne Michael Norgrove a Landan shekara uku da ta wuce.