Za a haramta wa Allardyce shiga harka kwallon kafa

Allardyce
Bayanan hoto,

Martin Glenn ya ce ba za a sassauta wa Allardyce

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila Martin Glenn ya ce mai yiwuwa a haramta wa Sam Allardyce shiga duk wata harkar kwallon kafa bayan an gano cewa badakalar da ta sa ya sauka daga kocin kasar.

Allardyce ya ajiye mukaminsa ne bayan jaridar the Daily Telegraph ta yi ikirarin cewa ya shaida wa wasu 'yan jarida da suka yi bad-da-kama a matsayin 'yan kasuwa cewa ya san "yadda za a iya kauce wa dokokin sayar da 'yan wasa".

A yanzu dai hukumar kwallon kafar ta Ingila tana jiran cikakkiyar shaidar jaridar ta wannan ikirari da ta yi kafin kafin ta dauki mataki kan tsohon kocin.

Glenn ya ce hukuncin da za a yi wa Allardyce zai kama daga cin sa tara zuwa haramta masa shiga harkokin wasanni.

Ya kara da cewa mai yiwuwa lamarin ya kai ga gurfanar da shi a gaban kotu.

Jaridar The Telegraph ta ce tana shirin mika wa 'yan sanda shaidu kan binciken da ta yi, ciki har da bincike kan zarge-zargen cin hanci a fannin kwallon kafar Ingila.