Kocin Ingila: Ana yi wa Wenger hannunka-mai-sanda

Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Glenn ya ce kocin Arsenal Arsene Wenger ya cancanci zama kocin kwallon kafar Ingila.

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila Martin Glenn ya ce kocin Arsenal Arsene Wenger ya cika dukkan ka'idojin zama kocin kwallon kafar kasar.

Kwantaragin kocin na Arsenal dai za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana, kuma ya ce a shirye yake ya zama kocin kwallon kafar Ingila.

Glenn ya kara da cewa hukumar bata kafe cewa sai lallai ya kasance dan Ingila ba ne kafin ya zama kocin kasar.

Sam Allardyce ya sauka daga kocin Ingila ne ranar Talata bayan an gano cewa ya ce ya san "yadda za a iya kauce wa dokokin sayar da 'yan wasa".

Allardyce ya ce ya yi matukar rashin jin dadin sauka daga mukaminsa, sannan ya nemi gafara bisa katobarar da ya yi.