Nigeria: Yaki da cin hanci ya fara a bangaren Shari'a

An hukunta alkalai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalai sun sha yanke hukunci mai daure kai

Hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a a Najeriya ta kori wasu manyan alkalai bisa samunsu da laifin cin hanci.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Mr Soji Oye ya sanya wa hannu ta ce hukumar ta kori babbar alkakin kotun jihar Kano, mai shari'a Kabiru Auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya da kuma babban alkalin kotun Enugu, mai shari'a I.A. Umezulike ne saboda laifukan da ke da alaka da karbar hanci.

Hukumar ta ce ta kori mai shari'a I.A. Umezulike saboda samunsa da karbar cin hanci game da batutuwan da suka shafi zaben kasar na shekarar 2015.

Hukumar ta ce shi ma mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya an same shi da laifin karbar hanci ne a kan zaben shekarar 2015.

Kazalika, an samu mai shari'a Kabiru Auta ne da laifin karbar fiye da N200m daga wajen wani dan kwangila Alhaji Kabiru Yakasai da zummar yi wa alkalin alkalan Najeriya da aka nada a wancan lokacin hanyar samun gida ta yadda shi kuma Alhaji Kabiru Yakasai zai samu kwangila daga wajensa.

Sanarwar ta kuma ce za a mika mai shari'a Kabiru Auta ga mataimakin babban sufeton 'yan sandan Najeriya shiyya ta daya da ke Kano domin a hukunta shi, sannan ta bukaci gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kore shi daga aiki.

Haka kuma ta bukaci gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya kori mai shari'a I.A. Umezulike daga aiki ba tare da bata lokaci ba, yayin da ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari sallami mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya daga aiki.

An sha zargin alkalan Najeriya da hannu a badakalar cin hanci, inda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarge su da yin kafar-ungulu a yakin da yake yi da rashawa cin hanci.