Hungary na zaben raba-gardama kan 'yan gudun hijira

Zaben raba-gardama a Hungary

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Viktor Orban na adawa da shirin

Al'umar kasar Hungary na yin zaben raba-gardama kan amincewa ko kin amincewa da shigar 'yan gudun hijira kasarsu bisa tilastawar tarayyar turai.

Firai minsitan kasar mai ra'ayin rikau Viktor Orban na adawa da shirin bai wa 'yan gudun hijira 160,000 damar shiga kasar.

Wata doka da tarayyar ta turai ta sanya a bara, sakamakon tuɗaɗar da 'yan gudun hijira suka yi zuwa turai, ta wajabta wa Hungary karbar masu neman mafaka akalla 1,294.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'ar kasar ta nuna cewa akasarin wadanda za su yi zaben ba sa kaunar 'yan gudun hijira su shiga kasar.

A lokacin da 'yan gudun hijirar ke tuɗaɗa zuwa Turai, Hungary ta zama wata hanya ta shigarsu kasashe irinsu Jamus.

Kasar ta rufe iyakokinta da Serbia da Croatia a yunkurin da ta yi na hana 'yan gudun hijirar shiga cikinta.

'Yan kasar sun yaba wa wannan mataki, kodayake kasar ta sha suka daga wajen kungiyoyin kare hakkin dan adam.