Birtaniya za ta fara shirin ficewa daga Turai a 2017

Theresa May

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Theresa May ta ce yana fatan komai zai tafi daidai

Firai Ministar Birtaniya Theresa May ta shaida wa BBC cewa a watan Maris na shekarar 2017 kasar za ta soma shirin ficewa daga tarayyar turai.

Mrs May ta ce tana fatan sauran kasashen tarayyar turai sun fara shirin zama ba tare da ita ba.

Firai Ministar ta yi alkawarin yin garambawul ga dokar da take yin tarnaki kan 'yancin da ɗaiɗaikun jama'a ke da shi a kasar.

Ta kara da cewa: "Yana da matukar muhimmanci ga Birtaniya da ma turai baki daya mu kammala batun ficewar mu ta yadda zai zama mai-wasa-lafiya ɗan-kallo-lafiya".