Za a daure manyan jami'an gwamnatin Iran

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Iran na son yin garanbawul kan albashin da manyan jami'anta ke dauka.
Hukumomin Iran sun ce za su daure manyan jami'an gwamnati kusan dari hudu kan yawan albashin da suke dauka.
Hakan ya biyo bayan wani bincike da aka gudanar, da ya gano manyan jami'an bankunan kasar su na daukar albashin da ya rubanya wanda kananan ma'aikata ke dauka da kusan sau hamsin.
Kakakin majalisar wakilan Iran Ali Larijani, shi ne ya yi magana akan ya na da kyau a yi garanbawul kan jami'an gwamnatin, dan kaucewa danne hakkin kananan ma'aikata a ma'aikatun gwamnatin kasar.