Sama da mutane100 ne suka mutu a Habasha

'Yan Habasha a lokacin da suke zanga zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane sama da 100 ne suka mutu a Habasha

Kafar yada labarai na Bloomberg, ya rawaito cewar sama da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a Habasha.

Bloomberg ya ce ,wani likita a wani asibiti a kasar Habashar, inda mutane da dama suka mutu, a lokacin da ake wata zanga zanga a wurin wani taron bikin al'adar gargajiya ne ya ce sama da mutane 100 ne suka mutu.

A baya dai Gwamnatin kasar ta ce mutane 52 ne suka mutu.

Mutane sun nutse a ruwa ko kuma an murkushesu har lahira a cewar Bloomberg.

Likitan ya kara da cewa mutane sun mutu ne a lokacin da suke tserewa daga motoci masu silke da aka yi amfani da su wajen tarwatsa cunkoson mutane.

Likitian, wanda ke garin Bishoftu da ke kasar Habashar, ya shaidawa Bloomerg cewar, "kusan mutane 100 ne suka mutu kuma mutane na cewa akwai da wasu mutanen da dama da suka nutse a cikin ruwa".

" Za a samu karin yawan mutanen da suka mutu. " Ya ce bai gawar wani wanda ya mutu sakamakon harbi ba.

Kasar Habasha dai ta fara alhinin kwanaki uku na mutanen da suka rasa rayukansu.