'Yan bindinga sun kwace wa Kardashian miliyoyin daloli

Kim Kardashin, tauraruwar Hollywood

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan bindinga sun kwace wa Kardashian miliyoyi

Wasu mutane biyu dauke da bindiga, wadanda suka saka kayan 'yan sanda sun yi wa Kim Kardashin sata a wani gida na masu hannu da shuni a birnin Paris, a cewar mataimakiyarta kan yada labarai.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya ce kayan da mutanen biyu suka sata, wanda akasarinsu sarkoki ne sun kai darajar $6.7m.

Mai kula da gidan ne ya raka masu bindigar, inda suka daure Kardashian a cikin bandaki, a cewar 'yan sanda.

Wata mai shekara 35, wadda ke magana da yawun Kim Kardashian, tauraruwar wasan talabijin na Hollywood da ke Amurka, ta ce Kim ta tsorata sosai, amma kuma ba su ji mata rauni ba.

Rahotanni dai na cewa, a halin yanzu tauraruwar ta bar kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito 'yan sanda na cewa, an sace akwatin ajiyar sarkoki wanda darajar sarkokin da ke cikinta, suka kai €6m har da zobe da darajarshi ta kai €4m.