'Yan Colombia sun yi watsi da kuri'ar raba gardama

'Yan Colombia a wajen kada kuri'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Colombia sunyi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya

Masu kada kuri'ar raba gardama a Colombia sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da tarihi da 'yan tawayen FARC a wani sakamako mai cike da al'ajabi na kuri'ar raba gardamar Colombia, inda sama da kashi 50 cikin 100 ba su amince da yarjejeniyar ba.

A makon da ya gabata ne dai shugaba Juan Manuel Santos da shugaban Farc Timoleon Jimenez, suka saka hannu a yarjejeniyar bayan an kwashe shekara hudu ana tattaunawa.

Sai dai, an bukaci amincewar 'yan kasar ta Colombia domin kafin ta fara aiki a hukumance.

A lokacin da ya ke wata sanarwa, shugaba Santos ya shadaiwa 'yan kasar cewa ya amince da sakamakon amma zai cigaba da aiki domin samar da kwanciyar hanakali.

A ranar Lahadi ne dai aka bukaci 'yan Colombia su kada kuri'ar su yarda, ko su yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiyar.