An kaddamar da littafin rayuwar Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamadou Issoufou , na Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Littafin tarihin rayuwar shugaba Muhammadu Buhari

An kaddamar da wani littafi a kan rayuwar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a Abuja, babban birnin kasar.

Farfesa John Paden, fitaccen malamin jami'an nan ne ya rubuta littafi wanda ya kunshi bayani a kan rayuwar shugaban da kuma gwagwarmayar da ya yi a siyasa ya zuwa yanzu.

Shugabannin kasashen Chadi da Benin da kuma Nijar masu makwabtaka da Najeriya sun halarci taron kaddamar da littafin.

Shugaban Niger, Mahamadou Issoufou dai ya iso Abuja ranar Lahadi domin hallartar taron kaddamar da littafin.

Littafin mai suna 'Muhammadu Buhari: Challenges of Leadership in Nigeria' wanda ke nufin kalubalen da ke tare shugabanci a Najeriya' yayi bayani a kan yadda rayuwar shugaba Buhari ta kasance tun daga lokacin da aka haife shi a shekarar alif dari tara da arba'in da biyu, da kuma irin mukaman da ya rike har ya zuwa yanzu.

Littafin ya kuma mai da hankali kan gwagwarmayar shugaban Najeriyar, musamman ma tsayawa takarar shugabancin kasa da ya yi ba tare da nasara ba a shekarar 2003 da shekarar 2007 da kuma shekarar 2011.

Wanda ya rubuta littafin wato Farfesa John Paden shi ne a shekarar 1986 ya rubuta tarihin marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello.