Rangers ta lashe Kofin Premier a Nigeria

'Yan kulub din Enugu Rangers
Bayanan hoto,

Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria

Enugu Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria na bana, bayan da ta ci El-Kanemi Warriors 4-0 a wasan mako na 38 da suka yi a ranar Lahadi.

Chisom Egbuchulum ne ya ci kwallaye uku rigis a karawar yayin da Osas Okoro ya ci kwallo daya.

Da wannan sakamakon Rangers ta lashe kofin da maki 63 a wasanni 38 da ta yi a bana.

Rabon da Enugu Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria shekara 32 da suka wuce, yanzu ta dauki na bakwai jumulla bayan da ta lashe a shekarar 1974 da 1975 da 1977 da 1981 da 1982 da kuma 1984.

Hakan kuma ya sa ta yi kan-kan-kan da Enyimba wadda ita ma tana da kofin Firimiyar Nigeria guda bakwai da ta lashe.