Ana cece kuce kan dage zaben Congo

'Yan sanda Jamhuriyyar Demokuradiyyar Congo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana cece kuce kan dage zaben Congo

A Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo an kasa cimma matsaya a tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan jam'yyar PPRD mai mulki da wasu wakilai daga wani bangaren 'yan adawa a kan dage zaben shugaban kasa zuwa watan Nuwamaba na shekarar 2018.

Hukumar zabe ta kasar ce ta gabatar da dagewar, amma wakilan 'yan adawa sun ce lokacin da aka kara ya yi yawa.

Ana tattaunawar ne dai a Kinshasa babban birnin kasar.

Babban jam'yyar adawa ta Etienne Tshisekedi, wato UDPF, da kuma wasu kungiyoyin farar hula masu fada a ji irin su National Episcopal Conference sun kaurace wa tattaunawar.

A cewar su tattaunawar ba ta kunshi kowa da kowa ba kuma suna tsoron wata kutungwila ce Shugaba Joseph Kabila yake shiryawa da nufin kara wa'adin mulkinsa ya zarta watan Dismaba na shekarar 2016, lokacin da wa'adin zai kare a karo na biyu kuma na karshe.