Masar: An harbe wani ƙusa a kungiyar 'yan uwa musulmi

Dan sandan Masar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Litinin da ta wuce ne ƙungiyar 'yan uwa Musulmi ta sanar da bacewar mamacin.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Masar ta ce, dakarun tsaro sun harbe wani ƙusa a ƙungiyar 'yan uwa Musulmai.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce Mohamed Kamal, da wani dan ƙungiyar sun mutu ne a wata musayar wuta a ranar Litinin din data wuce.

Ma'aikatar ta ƙara da cewa Mista Kamal ne ya jagoranci wani ɓangare na ƙungiyar na masu dauke da makamai, duk da cewa ƙungiyar na cewa ta zaman lafiya ce.

A baya-bayan nan sau biyu ana yanke wa Mohamed hukuncin daurin rai da rai.

A ranar Litinin da ta wuce ne ƙungiyar 'yan uwa Musulmi ta sanar da bacewar mamacin.