Ko azumi na ƙara wa mutum kuzari lokacin aiki?

Azumi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ko azumi na ƙarawa mutum kuzari a wajen aiki?

Yin azumi akai-kai wanda ya zama jiki da ake yi a matsayin wata hanya ta rage ƙiba,ko ya na taimakawa wajen ƙara maka kuzarin aiki a cikin mako?

Al'adar nan ta yin azumi ta zama jiki musamman irin wanda wasu mutane ke yi inda suke takaita cin abincin da ke sa ƙiba na wasu kwanaki.

Irin waɗannan mutunen su kan yi gwajin azumi na sa'o'i daban-daban kamar azumi daga sa'o'i 36 ko mafi tsanani wato sa'o'i 60 suna azumin.

Akwai wasu shaidu da suka nuna cewa taƙaita cin abinci da ke sa ƙiba yana da illa ta fuskar kiwon lafiyar mutum a nan gaba wadanda suka haɗa da ƙarfafa yanayi da kuma samun ingantaccen barci.

Sai dai wasu ma'aikata a California sun zaɓi wani ɓangaren da yake da fa'ida a al'adar inda suka ce a ranakun da basa cin abinci sun fi yin aiki a sosai a ofisoshinsu.

Sun ce sun fahimci cewar sun fi samun kuzari da kaifin tunani a lokutan da su ke aiki suna kuma azumi.

Waɗannan mutane da ke kiran kan su WeFast wasu abokai ne a shafin Internet da suka yi amannar cewa jirkita tsarin kiwon lafiyar dan adam zai iya haddasa ƙarin lafiya da kuma samun ingantaccen rayuwa.

Sun yi gwaji na sa'o'i daban daban daga sa'o'i 36 na dakatar da cin abinci zuwa mafi tsanani wato sa'o'i 60 suna azumi.

Wasu kuma sun bi sahu inda suka yi azumin na sa'o'i 23 a rana.

Manufar dai ita ce su tantance yadda azumin su ya kasance daga ƙarshe.

Hakkin mallakar hoto Peter Bowes
Image caption Mambobin kungiyar WeFast suna haɗuwa duk ranar Laraba domin yin buɗe baki

A birnin San Francisco ne dai wani kamfani mai suna Nootrobox ya ɓullo da tsarin azumin WeFast.

Kamfanin yana yin wasu ƙwayoyi ne na ƙara kuzari da ake kira nootropics da ke ƙara kaifin basira.

Yin azumi na daga cikin al'adar kamfanin, ko da ya ke ba wajibi ba ne, amma kusan kowa a ciki tawagar ta mutum 13 yana yi azumin a ranar Talata.

A ranar laraba da safe ne kuma su kan haɗu da sauran 'yan ƙungiyar WeFast mai mambobi kimanin 1,200 domin yin buɗe baki.

Ana dai yin buɗe bakin ne a wurin shan shayi da ke cikin unguwanni, inda mambobin ƙungiyar kan yi wa juna bayani game da yadda su ka ji a lokacin da su ke azumin.

"Babban abu da ya faru da ni da kuma mutane da dama a wannan ƙungiyar shi ne na tunanin ƙara himma a wajen aiki," in ji Geoff Woo, shugaban kamfanin Nootrobox.

Mai yiwuwa akwai wani abu da suka ci ko kuma suka sha.

Sai dai bincike da aka gudanar sun gano cewa nau'o'in azumi daban daban yana matukar tasiri ga jikin dan adam.

Yayin da hujjoji akan tasirin da azumi ke yi a kan ayyuka ba lallai ne ya zama gaskiya ba, mutane da dama wadanda su ke bin al'adar yin azumin sau da ƙafa- kamar rahoton mambobin kungiyar WeFast da ke cewa sun lura da yadda suka samu ƙarin himma, kamar yadda masu tseren wasanni su kan ji.

Bincike da aka gudanar a ɗakunan bincike sun nuna cewa wasu sauye sauye na sinadarai da ake samu a ƙwaƙwalwa sune ke janyo hakan.

Mark Mattson, Farfesa ne fannin ƙwaƙwalwa a jami'ar Johns Hopkins wanda ya ce binciken sa ya nuna cewa suna ƙara yanayin tunani.

Ana dai zaton cewa mutane da su ke jin ƙarin kuzari a lokacin da suka fara ƙona kitse a jikin su maimakon abinci da ke sa mutum ƙiba, in ji Dr Eric Verdin wani mai bincike a cibiyar Gladstone dake birnin San Francisco.

Sai dai azumi yana da haɗari ga wasu mutane musamman mata masu ciki ko kuma waɗanda ke shayar da jarirai, ko kuma masu cutar suga wato diabetes da wasu cututtuka masu nasaba.

Domin a duk lokacin da jiki ya gaji, kuma aka taƙaita masa samun abinci mai gina jiki, lamarin ka iya yin muni.

A don haka ga duk wani da ke da sha'awar yin azumi irin wanda masu bincike akan lafiyar dan adam a San Francisco wato 'biohack', zai fi kyau ya tuntubi likitan sa tukuna.

Idan kana son karanta wannan labari a harshen Ingilishi latsa nan: Can giving up food make you work better?

Labarai masu alaka